Isa ga babban shafi
China

An wayi gari babu wanda ya mutu a China

Wasu mutanen yankin Wuhan na China na gudanar da hada-hadarsu ta yau da kullum
Wasu mutanen yankin Wuhan na China na gudanar da hada-hadarsu ta yau da kullum REUTERS/Aly Song

A karon farko cikin watanni 3 China ta yi nasarar ganin kwana guda ba tare da samun ko da mutum guda da cutar coronavirus ta kashe ba, nasarar da ke zuwa kwana guda gabanin gwamnati ta bai wa al'ummar yankin Wuhan izinin komawa harkokinsu na yau da kullum.

Talla

Wannan na nuna irin namijin kokarin da China ta yi a yaki da annobar COVID-19 ko kuma coronavirus wadda kawo yanzu ta hallaka fiye da mutum dubu 75 sassan duniya.

Sai dai sanarwar  da China ta fitar na zuwa ne daidai lokacin da zargi ke kara karfi a kanta kan cewa tana boye hakikanin adadin mutanen da suka kamu da cutar a kasar, da wadanda cutar ta kashe, zargin da gwamnatin kwamunisancin kasar ta China ke ci gaba da musantawa.

Fiye da watanni 2 al'ummar lardin Hubei suka shafe kulle a gidajensu karkashin dokokin yaki da coronavirus wadda ta samo asali daga yankin Wuhan, babbar birnin lardin mai kunshe da tarin baki, yayin da wasu al'ummar yankin na Wuhan da ke rayuwa a wasu sassa na China suka fara komawa gida bayan sassaucin cutar.

Sai dai kuma hankula sun tashi bayan da aka fara samun alamomin cutar jikin wasu baki da suka koma yankin na Wuhan.

Daga tsakar daren yau Talata ne dai dokar bai wa mutanen sukunin fara hada-hadar yau da kullum za ta fara aiki, sai dai mai magana da yawun gwamnatin yankin na Wuhan ta ce, har yanzu akwai sauran dokoki ciki har da takaita sufurin fita ko kuma shigowa yankin.

Al'ummar yankin dai na ci gaba da farin cikin maraba da matakin na gwamnati, sai dai jami'an lafiyar yankin na ganin har yanzu akwai sauran aiki a gaban gwamnati yayin da suka shawarci al'umma kan yin taka-tsan-tsan a hada-hadar jama'a ko kuma shiga cunkoso.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.