Isa ga babban shafi
Coronavirus-Faransa

Coronavirus ta harbi jirgin yakin Faransa

Jirgin dakon jiragen yakin Faransa da ke kan tekun Atlantica
Jirgin dakon jiragen yakin Faransa da ke kan tekun Atlantica Reuters

Katafaren jirgin ruwan dakon jiragen saman yakin Faransa da ke kan tekun Atlantica, ya yanke shawarar gaggauta komawa gida Faransa bayan an gano sama da mutane 40 da suka kamu da cutar coronavirus, wadanda tuni aka killace su a cikin jirgin.

Talla

Ofishin Ministan Aikin Sojin kasar ya ce, mutanen da suka harbu da cutar suna karkashin kulawar likitoci kuma ba sa fuskantar wata mummunar damuwa.

Sanarwar ofishin Minstan Ayyukan Sojin Faransa ta tabbatar cewa, tawagar likitoci masu aikin gwajin cutar tare da kayayyakin aiki na kan hanyar isa ga jirgin, domin kula da wadanda suka kamu tare da hana yaduwar kwayar cutar a cikin jirgin.

Sai dai wata majiyar sojin Faransa ta ce, katafaren jirgin dokon jiragen yakin na kunshe da duk kayayyakin kiyon lafiyar da ake bukata da zai iya ba shi damar ci gaba da aikin da ke gabansa.

Tun ranar 21 ga watan Janairu, jirgin mai aiki da nukiliya da ke tekun Atlantica a gabar ruwan kasar Portugal, ya kawo karshen ran-gadinsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.