Isa ga babban shafi
Coronavirus

Coronavirus ta kashe Amurkawa kusan dubu 2 a kwana guda

Shugaban Amurka Donald ya yi barazanar zabtare tallafin da kasar ke bai wa Hukumar Lafiya ta Duniya saboda zargin ta da nuna wa China goyon baya
Shugaban Amurka Donald ya yi barazanar zabtare tallafin da kasar ke bai wa Hukumar Lafiya ta Duniya saboda zargin ta da nuna wa China goyon baya REUTERS/Tom Brenner

Amurka ta yi asarar mutane kusan dubu 2 a cikin sa'o'i 24 da suka gabata sakamakon cutar coronavirus wadda a jumulce, ta lakume rayuka dubu 12 da 21 a kasar kadai, yayin da shugaba Donald Trump ya yi barazanar zabtare kudaden da Amurka ke bai wa Hukumar Lafiya ta Duniya saboda zargin ta da nuna wa China goyon baya.

Talla

Shugaba Trump  ya zargi Hukumar Lafiyar ta Duniya da nuna goyon baya ga China wadda ta dage haramcin hana zirga-zirga a birnin Wuhan, makyankyasar annobar coronavirus.

A cewar Trump, kamata ya yi Hukumar Lafiyar ta Duniya WHO ta caccaki matakin China na janye dokar hana zirga-zirgar.

Trump ya shaida wa manema labarai a birnin Washington cewa, zai zabtare kaso mai yawa daga cikin kudaden da Amurka ke bai wa hukumar WHO.

Amurka ce kasar da ke kan gaba wajen bai wa hukumar tallafin kudaden gudanar da ayyukanta.

Kasar China ta bada rahoton cewa, an wayi gari ba tare da samun mutun ko guda da coronavirus ta kashe a Wuhan ba a daidai lokacin da ita Amurka ta rasa mutane kusan dubu 2 a kwana guda.

Kodayake shugaba Trump da wasu kasashen duniya sun bayyana shakkunsu kan alkaluman da China ke bayarwa dangane da mace-macen da take samu a sanadiyar coronavirus, inda suke ganin cewa, tana boye bayanan gaskiya.

A bangare guda Hukumar Lafiyar ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce,  adadin mutanen da suka mutu sakamakon cutar COVID-19 ya zarce 80,000, yayin da cutar ta ratsa kasashe 192 na duniya.

Alkaluman Hukumar Lafiya sun ce, mutane miliyan guda da dubu 397,180 suka kamu da cutar a kasashen duniya 192, yayin da ta kashe 80,142, kana 257,100 suka warke.

Italiya ke matsayi na farko da mutuwar mutane 17,127 daga cikin mutane 135,586 da suka kamu, sai Spain da ta gamu da mutuwar mutane 13,798 daga cikin 140,510 da suka kamu, sannan Amurka mai mutane 12,021 da suka mutu daga cikin 383,256 da suka kamu.

Kasar Faransa ta zama kasa ta 4 da ta samu mutuwar mutane sama da 10,000, sakamakon samun adadin mutane 10,328 daga cikin mutane 109,069 da suka kamu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.