Isa ga babban shafi
Coronavirus

Mamatan coronavirus karuwa suke yi kullum

Coronavirus ta doshi lakume rayuka dubu 85
Coronavirus ta doshi lakume rayuka dubu 85 indiatimes

Sama da mutane dubu 82 sun rasa rayukansu a sanadiyar cutar coronavirus da ta bulla a kasashen duniya 192. Daga cikin mamatan har da mutane kusan dubu 2 da wannan cuta lakume rayukansu cikin sa’o’i 24 a Amurka kadai.

Talla

Ya zuwa tsakiyar ranar wannan Laraba, an tabbatar da mutuwar mutane dubu 82 da 721 bayan sun kamu da cutar coronavirus.

Annobar ta kashe mutane kimanin dubu 17 da 127 a Italiya kadai, kasar da ta fi fama da wannan bala’in a nahiyar Turai.

Spain ce kasa ta biyu da ta yi asarar mutane dubu 14 da 555, sai kuma Amurka wadda ta yi asarar jumullar mutane dubu 12 da 911.

A cikin sa’o’i 24, Amurkar ta rasa mutane dubu 1 da 939 kamar yadda jami’ar Johns Hopkins ta sanar.

Faransa kuwa ta yi asarar mutane dubu 10 da 328, inda a Birtaniya coronar ta kashe mutane dubu 6 da 159.

Fiye da mutane miliyan 1 da dubu 400 ne dai suka kamu da coronavirus mai toshe hanyoyin numfashi kamar yadda alkaluman hukumomin kasashen duniya suka nuna.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.