Isa ga babban shafi
Coronavirus

Sama da mutane biliyan 1 za su rasa aiki saboda coronavirus

Wasu ma'aikatan kamfani a birnin London
Wasu ma'aikatan kamfani a birnin London arstechnica

Majalisar Dinkin Duniya ta ce, yanzu haka annobar coronavirus na barazanar raba kimanin mutane biliyan 1 da miliyan 250 da guraben ayyukansu. Tun yakin duniya na 2 raban da aka irin wannan masifar.

Talla

Cikin sabon rahoton da ta wallafa, Hukumar Kwadago ta Majalisar Dinkin Duniya, ta yi gargadin cewa, ci gaba da yaduwar annobar coronavirus da kuma tsauraran matakan da gwamnatoci ke dauka domin dakile ta, zai janyo tafka hasarar kashi 6.7 cikin 100 na sa’o’in ayyuka a fadin duniya a shekarar 2020, wato kwatankwacin rasa guraben ayyukan yi na din-din-din miliyan 195.

Wannan rahoto na zuwa ne a daidai lokacin da yawan wadanda suka kamu da cutar coronavirus a fadin duniya ya zarta miliyan 1 da dubu 350, ciki har da wasu mutanen sama da dubu 80 da annobar ta halaka.

Binciken Hukumar Kwadagon ta Majalisar Dinkin Duniya ya kuma ce, ma'aikatan da ke yankin Asiya da Pacific, za su fi kowanne yanki a duniya fuskantar barazanar rasa guraben ayyukansu, inda a yanzu haka adadin ma'aikata a kalla miliyan 125  ke cikin hadarin rabuwa da ayyukansu a Asiyan da Pacific.

Wata sabuwar matsalar da ta kunno kai ita ce karuwar yawan marasa aikin yi a duniya da adadinsu ya kai miliyan 25 a shekarar nan kadai, duk dai dalilin tasirin annobar murar ta COVID-19.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.