Isa ga babban shafi
Muhallinka Rayuwarka

Chanjin yanayi

Sauti 10:00

Chanjin yanayi ko dumamar sa, batu ne dake cigaba da haddasa zazzafar muhawara da musayar ra'ayi tsakanin masana da kwararraru,musamman kan illolin da wannan batun zai haifar a rayuwar bil adama a doron kasa. Tuni dai wani taron kasa-da-kasa a birnin Copenhegen na Denmark,yayi kasedi cewa dole kowacce kasa ta tanadi yadda zata tunkari wannan batu na chanji yanayi daya fara bayyana a ambaliyar ruwan sama da kuma karancin sa a wani bangare na duniya bisa wasu dalilai.Sai dai kuma kamar yadda bincike ya nuna a Nigeria kamar sauran kasashe masu tasowa inda wannan matsala ta chanji yanayi tafi bayyana,galibin jama'a basu san wannan batu ba,balle ma suyi la'akarin yadda zasu bullo masa. Wannan jahilcin dake bayyana game da batun na chanjin yanayi,yasa al'umma na cigaba da gurbata muhalli ba tare da sanin illolin da wannan gurbatar ke haifarwa ba.Watakila dai chunkoson abubuwan hawa a birane dake fitar da gubataccen iska/hayaki da kuma musamman sarar itatuwa a matsayin makamashi,sune kan gaba wajen haifar da matsalolin gusowar hamada,zaizayar kasa da kuma yanayin dake barazana ga tsirrai ko yabanya. Wadannan sune mayan kalubalen da galibin kasashe masu tasowa ke fuskanta,kalubalen samun makamashi mai sauki domin rage chi iyakar da kullu yaumin ake wa dazuzzuka wajen neman itace girki.A yayin da hukumomi musamman a Nigeria ke dawainiyar binciken wasu hanyoyi na samun makamashi mafi sauki da arha,bincike ya nuna cewa sana'ar itace da yin gawayi,na cigaba da bunkasa a yawanci jihohi da kananan hukumomi duk kuwa da cewa akwai dokar dake tsawatawa kan haka. 

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.