Isa ga babban shafi
Morocco

Hatsarin Jirgin Sama Ya Kashe Mutane 78 A Morocco

Taswirar kasar Morocco
Taswirar kasar Morocco RFI

Mutane akalla 78 ne suka rasa rayukansu, wasu mutane 3 suka sami raunuka sakamakon wani hatsarin jirgin sama na Sojan kasar Morocco a tsaunukan kasar.Jirgin saman kirar Hercules C-130 ya afka tsaunukan kasar ne cikin wani yanayi mara kyau.Jirgin na sintiri ne tsakanin garin Agadir zuwa Laayoune dake Yammacin Sahara dauke da maaikata shida, sojoji 60 da fararen hula 12 lokacin da ya fadi.Hukumomin kasar sun danganta hatsarin ga rashin kyawun yanayi. 

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.