Isa ga babban shafi
Duniya

Za a fuskanci rikice-rikice a 2018

Rahoton ya ce za a cigaba da samun rikice-rikice a wasu sassa na duniya.
Rahoton ya ce za a cigaba da samun rikice-rikice a wasu sassa na duniya. Reuters/Feisal Omar

Wani rahoto da kungiyoyin masana suka fitar ya yi hasashen cewa cikin shekara mai kamawa ta 2018, za a samu yawaitar yake-yake da yunwa, wadanda za su yi matukar barazana ga dan'adam.

Talla

Rahotan na wata kungiyar masana mai zaman kanta mai mazauninta a Geneva, ACAPS a takaice na ayyukan agaji da sa idanu kan kasashen duniya 150, ta yi hasashen yadda abubuwa za su kasance ne cikin shekara ta 2018 a kasashe 18 na duniya, kuma ta gano cewa akwai matsalar gaske.

Rahoton wanda kamfanin dillancin labaran Reuters ya wallafa, na cewa idan har hasashen na nuna wannan shekara mai karewa babu kyau, to zai iya shafan abubuwan da za su wakana shekara mai kamawa.

Rahoton na nuna matsalar rashin tsaro da rikice-rikice za su cigaba a kasashe irin su Afghanistan, da Jamhuriyar Democradiyyar Congo, da Libya, da Habasha, da Mali, da Somalia, da kuma Syria.

A cewar wannan rahoto a shekara mai kamawa kasar Habasha za ta bi sahun irinsu Arewa-maso-gabashin Najeriya, da Somalia, da Sudan ta kudu da Yemen, a matsayin wuraren da ke da hatsarin fadawa cikin matsanancin karancin cimaka,

Duk da cewa an karya lagon kungiyar IS ta masu jihadi a Iraqi, rahoton ya yi  hasashen cewa rage-ragen ‘yan wannan kungiya da ke wasu kasase za su rika kai hare-haren sari-ka-noke.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.