Isa ga babban shafi
Ilimi Hasken Rayuwa

Za'a ba 'Yan kasa da shekaru 13 damar fara amfani da Facebook

Sauti 09:31
Yara kanana a saman Kwamfuta suna mu'amula da shafin Facebook
Yara kanana a saman Kwamfuta suna mu'amula da shafin Facebook GeeksClub.com

Shafin Zumunta na Facebook a Intanet ya fara nazarin fasahar da yara kanana ‘Yan kasa da shekaru 13 zasu fara amfani da shafin karkashin kulawar iyayensu domin basu damar sada zumunci a shafin mai yawan mutane Miliyan 900.

Talla

Wasu Rahotanni masu karo da juna sun bayyana kalubalen da ke gaban Facebook akan batun tantance shekarun masu amfani da shafin.

Masana suna ganin ya zama dole sai Facebook ya yi la’akari da dokokin kare hakkin kananan yara na Amurka da sauran kasashen Duniya.

Wani bincike da Kamfanin Microsoft ya gudanar yace akwai yara kannana da dama da ke amfani da shafin Facebook kafin wannan yunkurin na basu dama karkashin kulawar iyayensu.

Shirin Ilimi hasken Rayuwa ya yi bayinai game da wannan batu tare da zantawa da Ben Mezrich shahararren maruci wanda ya rubuta littafi na musamman game da rayuwar shugaban Kamfanin Facebook, Mark Zuckerberg.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.