Isa ga babban shafi
Amurka

Monsanto zai biya diyyar miliyoyin Dala a Amurka

Wata mata na amfani maganin Roudup na kamfanin Monsanto wajen kashe kwarin da ke cinye amfanin gona
Wata mata na amfani maganin Roudup na kamfanin Monsanto wajen kashe kwarin da ke cinye amfanin gona REUTERS/Benoit Tessier

Wata kotu a Amurka ta umarci Kamfanin Sarrafa Magungunan Kashe Kwarin Kayayyakin Gona, wato Monsanto, da ya biya diyyar Dala miliyan 80 ga wani Ba’amurke da ya dora laifin kamuwa da cutarsa ta Kansa kan amfani da maganin Roundup da kamfanin ke samarwa.

Talla

Alkalan kotun ta birnin San Francisco sun samu kamfanin na Monsanto da laifin sakaci wajen yi wa jama’a gargadi game da illar da ke tattare da maganinsa na Roundup, abinda ya sa alkalan suka umarci kamfanin da ya biya Edwin Hardeman diyyar Dala miliyan 80 baya ga wata Dala dubu 200 na daban da ya kashe wajen neman lafiyarsa.

A karo na biyu kenan a ‘yan kwanakin nan da Monsanto ke fuskatar hukuncin kotu, in da a wata shari’ar ta daban, kotun California ta bukace shi da ya biya wani mutun miliyoyin kudi na Dala bayan shi ma ya kamu da cutar Kansa a dalilin maganin.

Ita ma kotun ta California ta samu kamfanin ne da sakacin gargadin illar da ke tattare da maganin.

Ana ganin watakila nan gaba a kara samun dimbin jama’a da za su fito don neman diyya saboda illar da maganin na Monsanto ya yi musu.

Matakin kotun babban koma-baya ne ga Kamfanin magunguna na Bayer da ya saye Monsanto a cikin watan Yunin shekarar bara akan farashin Dala biliyan 63.

Tuni hannayen jarin kamfanin na Bayer ya fadi a jiya Alhamis da kashi 1.12 a birnin Frankfurt na Jamus, yayinda ya ce, zai daukaka kara duk da cewa, ya nuna damuwa kan illar da maganin ya yi wa Ba’amurken.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.