Isa ga babban shafi
Nijeriya

An sako dan kasar Britaniya da aka yi garkuwa da shi a NiJeriya

Taswirar Nijeria na nuna birnin Lagos
Taswirar Nijeria na nuna birnin Lagos © RFI

Rahotanni daga Najeriya na nuna cewa an saki mutumin nan, dan kasar Birtaniya wanda wasu mutane dauke da makamai suka yi garkuwa da shi a birnin Legas dake kudancin kasar.A wata sanarwa da Ofishin Jakadancin Birtaniya ya fitar, dauke da sa hanun Kakakin ofishin, Wale Adebajo ta bayyana cewa an saki mutumin, sai dai sanarwar ba ta ambaci ko an biya kudin diyya kafin sako mutumin ba.A ranar ranar Talatar da ta gabata ne aka yi garkuwa da mutumin wanda ba a bayyana sunansa ba. 

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.