Isa ga babban shafi
Najeriya

Batun sace ‘Yan Mata ya mamaye Twitter da Facebook

Uwar gidan Shugaban Amurka Michelle Barack Obama dauke da sakon "A dawo muna da 'Yan Matanmu" da aka sace a Najeriya
Uwar gidan Shugaban Amurka Michelle Barack Obama dauke da sakon "A dawo muna da 'Yan Matanmu" da aka sace a Najeriya divulgação/Casa Branca

Batun sace ‘Yan mata a Chibok ya mamaye dandalayen zumunta Facebook da Twitter, wanda hakan ke nuna duniya ta damu da ‘Yan mata sama da 200 da Mayakan Boko Haram suka sace a Najeriya sama da makwanni uku.

Talla

Shafin Intanet na Topsy.com da ke gudanar da bincike a dandalayen zumunta yace an yada maudu'in “ A dawo muna da ‘Yan Matanmu” har sau Miliyan daya da dubu dari takwas a Twitter.

Kuma a ranar Alhamis kawai an yada batun dawo da ‘Yan matan a Twitter sau 412,000 fiye da adadin ranar 14 ga watan Afrilu da aka sace ‘Yan matan.

Uwar gidan Shugaban Amurka, Michelle Obama tana cikin wadanda suka aiko da sakon addu’ar neman a saki Matan.

Akwai kuma Anne Hathaway da Angelina Jolie, Fitattun ‘Yan Fim a Amurka cikin wadanda suka bayyana alhininsu.

Shafin Facebook kuma na “A dawo muna da ‘Yan matanmu” ya samu masoya (Likes) 94,000. Shafin Fadar White house da ke kira ga Shugaban Amurka Barack Obama ya taimakwa Najeriya ya samu mabiya 21,000.

A cikin Sakon Bidiyo, Shugaban Boko Haram ya fito yana ikirarin sace ‘Yan Matan sama da 200 wadanda ya danganta a matsayin bayi tare da shan alwashin zai yi masu aure.

Wannan yekuwar a Shafukan Intanet ya sa Amurka da Faransa da Birtaniya suka yi alkawalin taimakawa Najeriya domin kubutar da matan daga Mayakan Boko Haram.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.