Isa ga babban shafi
Nijar

Cutar murar Tsuntsaye ta bulla a Maradi

Cutar Murar tsuntsaye ta  H5N1 ta bulla a Najeriya da Nijar
Cutar Murar tsuntsaye ta H5N1 ta bulla a Najeriya da Nijar Reuters

Hukumomin Jamhuriyar Nijar sun sanar da barkewar cutar murar Tsuntsaye, a wasu yankuna da ke arewaci kasar na garin Maradi, da ke kan iyaka da Najeriya. Tuni dai aka kebe gonaki da lamarin ya auku, tare da daukar matakan hanna shige da ficen kaji a garin.

Talla

Hukumomin lafiya a Nijar yanzu haka suna jiran sakamakon gwaji da aka tura zuwa Italiya.

Daraktan kula da lafiyar dabbobi a Maradi Isyaku Salihu ya ce cikin kwana biyu kaji kusan 800 suka mutu, akan haka ne suka fara daukar matakai.

A bana an samu bullar cutar a Jihohin Kano da Lagos a Najeriya, kuma rahotanni sun ce cutar da bulla Burkina Faso.

Ma’aikatar kula da dabbobi ta dauki matakin haramta shigo da kaji daga kasashen da ke fama da cutar.

Cutar dai na yaduwa zuwa ga bil adama idan ba a yi gaggawar daukar matakai ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.