Isa ga babban shafi
Najeriya-Boko Haram

Sojan Najeriya sun kama masu samarwa 'yan Boko Haram miyagun kwayoyi

Wasu sojojin Najeriya
Wasu sojojin Najeriya (Photo : AFP)

Rundunar sojan Najeriya ta sanar da cafke wasu mutane, da ke samar wa ‘yan Boko Haram da miyagun kwayoyi da sauran kayan shaye-shaye.

Talla

Rundunar sojan tace an cafke mutanen ne a tsakanin garin Depchi da kuma Giedan da ke jihar Yobe daya daga cikin yankunan da ‘yan Boko Haram suka dade sun cin karensu ba babbaka.
Sanarwar da kakakin rundunar sojan kasar Kanar Sani Usman Kukasheka ya fitar, ta bayyana cewa an cafke mutanen ne a jiya talata lokacin da jami’an tsaro ke gudanar da bincike a motocin da ke zirga-zirga a yankin.
Kanar Kukasheka ya kuma ce baya ga miyagun kwayoyin, rundunar sojan ta kuma sami man da ake amfani dashi a injina.
Rundunar sojan, da bata bayyana yawan mutane data kama ba, tace miyagun kwayoyin da aka kama sun tabatar da cewa, ba gaskiya cikin ikirarin da ‘yan Boko Haram keyi na neman kafa daular Islama.
Addinin Islama dai ya haramta amfani da miyagun kwayoyi.
Rikicin Boko Haram yayi sanadiyyar rasa ran a kalla mutane 15,000, wasu fiye da Miliyon daya suka tsere daga gidajensu cikin shekaru 6 da suka gabata.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.