Isa ga babban shafi
Najeriya

Dakarun Najeriya sun lalata sansanonin 'yan Boko Haram

wasu sojojin Najeriya a bakin daga
wasu sojojin Najeriya a bakin daga AFP PHOTO/SUNDAY AGHAEZE

Rundunar sojan Najeriya ta ce a halin yanzu ta lalata illahirin sansanonin da ‘yan Boko Haram suka kafa a yankin arewa maso gabashin kasar, abinda ke tabbatar da cewa kungiyar kuma ba za ta sake yunkurin kama wani yankin na kasar ba.

Talla

A ganawarsa da manema labarai a birnin Abuja, kakakin ma’aikatar tsaro Najeriya Kanar Rabe Abubakar, ya ce dakarun kasar na amfani da sojan sama da na kasa, domin tabbatar da cewa sun isa a inda ‘yan kungiyar ta Boko Haram ke boye, kuma sun yi nasarar kama da dama daga cikinsu.

A wani bangaren kuma, rundunar sojan Najeriya ta 7 da ke Maiduguri a jihar Borno, ta saki mutane 128 da suka share tsawon lokaci tsare bisa zargin cewa ‘yan kungiyar Boko Haram ne.

Babban hafsan sojan kasa na Najeriya Lafnal janar Tukur Buratai ne ya jagoranci bikin mika wadannan mutane ga hukumomin jihar ta Borno, kuma bayan danka su a hannun mahukuntan jihar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.