Isa ga babban shafi
Najeriya

Kungiyoyin kwadagon Najeriya suna so a zartar da hukuncin kisa kan masu cin hanci

asu 'yan kungiyar Kwadagon Najeriya suna  zanga zanga
asu 'yan kungiyar Kwadagon Najeriya suna zanga zanga © Reuters/Akintunde Akinleye

Manyan kungiyoyin kwadago a Najeriya NLC da TUC da wasu kungiyoyin fararen hula, sun bukaci a samar da dokar zartar da hukuncin kisa, kan wadanda aka sama da laifin rashawa kamar dai yadda kasashen China da India ke yi.

Talla

Kungiyoyin sun yi wannan kira ne a wani taron manema labarai na hadin gwiwa da suka gabata a jiya laraba a birnin Abuja, inda suka bayyana cewa dole ne gwmanatin ta samar da doka mai tsanani domin samun nasarar yakin da rashawa a kasar.

Kungiyoyin sun bayyana goyon bayansu ga shirin shugaban kasa Muhammadu Buhari na yaki da cin hanci da rashawa, inda suke shirin wani gangamin goyon bayan hakan, yau a birnin Abuja.

Shugaban kungiyar kwadagon kasar Ayuba Wabba, yace kungiyar na goyon bayan duk wani matakin da shugaban zai dauka a wannan bangaren.
Shugaban kungiyar Kwadagon ya nemi gwamnatin tarayyar kasar ta tabbatar da bin sawun dukkan kudaden da aka sace daga kasar, don a dawo dasu, tare da hukunta masu hannu a ciki.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.