Isa ga babban shafi
Najeriya-Kogi

APC za ta tsayar da sabon dan takara a Kogi

Jam’iyyar APC a Najeriya ta ce zata gudanar da zaben fidda gwani dan samo wanda zai maye gurbin tsohon dan takaran gwamnan jihar Kogi Abubakar Audu da Allah Ya yiwa rasuwa ranar lahadi.

Talla

Shugaban Jam’iyar John Oyegun ya bayyana haka ga manema labarai sakamakon karbar takardar dake bukatar haka daga hannun hukumar zaben kasar wadda ta bukaci mika mata sunan wanda zai maye gurbin marigayin.

Hukumar zaben kasar ta sanar da cewar za ta sake gudanar da zabe a mazabu 91 da ta soke ranar 5 ga watan Disamba mai zuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.