Isa ga babban shafi
Najeriya-Kano-Kebbi

Gobara a kasuwanni Sabon gari dake Kano da babban kasuwa ta Kebbi

Gobara kwanankin Baya a kasuwar Singa dake Kano
Gobara kwanankin Baya a kasuwar Singa dake Kano

Rahotanni daga jihohin Kano da Kebbi da ke Najeriya na cewa wata gobara ta tashi a baban kasuwan Birnin Kebbi da ta Sabon gari dake Kano inda akayi asaran dimbin dukiyoyi.

Talla

Bayanai daga Kano sun ce gobarar ta tashi ne tun tsakiyar daran jiya kuma har yanzu an gaggara kashe ta, kazalika a Kebbi inda aka rawaito cewa kusan kasha 80 cikin 100 na kusuwar ta kone kurumus.

Har yanzu dai babu cikakkun bayanai dangane da musababbin tashin Gobarar, kana babu rahota asarai rai ko rauni zuwa wannan lokaci.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.