Isa ga babban shafi
Najeriya

Gwamnonin Najeriya za su sa ido kan man fetir

Ana zargin wasu da karkatar da man fetir daga Najeriya zuwa kasashen Kamaru da Chadi don samun kudi
Ana zargin wasu da karkatar da man fetir daga Najeriya zuwa kasashen Kamaru da Chadi don samun kudi Getty Images/Suzanne Plunkett

Gwamnatin Najeriya ta bukaci gwamnonin jihohin kasar 36 da su sa ido kan yadda ake rarraba man fetir a jihohinsu, a wani mataki na kokarin kawo karshen matsalar karancin mai a duk fadin kasar.

Talla

Wannan na zuwa ne bayan shugaba Muhammadu Buhari ya gana da karamin ministan mai, Dr. Ibe Kachikwu wanda ya ce, wasu na karkatar da kashi 30 cikin 100 na man zuwa kasashen Kamaru da Chadi don samun kudi.

An dai bukaci gwamnonin da su kafa wata runduna da za ta rika sa ido akan yadda ake jigilar mai daga matattaransa zuwa wurare da dama domin taimaka wa gwamnatin tarayya a yaki da ta ke yi da masu boye man da kuma karkatar da shi.

Gwamanti na son gudanar da bincike don sanin inda ake kai man, abinda ya sa ta bukaci gwamnonin da su zura ido a koda yaushe kan harkokin man a jihohinsu.

Matsalar mai dai ta ki ci ta ki cinye wa a Najeriya, abinda ya jefa ‘yan kasar cikin mawuyacin halin rayuwa.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.