Isa ga babban shafi
Najeriya

Manoma sun yi taro kan makomar arzikin Najeriya

Shugaban Najeriya  Muhammadu Buhari da takwaransa na Faransa, Francois Hollande
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da takwaransa na Faransa, Francois Hollande AFP PHOTO / DOMINIQUE FAGET

Kungiyoyin manoma a karkashin hadin kan kasashen Faransa da Najeriya sun gudanar da wani taro a birnin Legas kan makomar Najeriya bayan arzikin man fetur, inda suka tattauna kan yadda za su hada kai domin inganta noma a kasar.

Talla

Taron wanda ya samu halartar manoma, masana da kuma jami’an bankuna, ya bukaci gwamnati ta samar da yanayi mai kyau ta yadda manoman za su samu kwarin gwuiwa wajen samun riba.

Najeriya dai na samun kimanin kashi 70 cikin 100 na arzikinta ne daga man fetir, yayin da masana da kwararru a fannin tattalin arziki ke ci gaba da kiran gwamnati da ta kara kaimi wajen farfao da harkar noma kamar yadda ta ke a can baya.

Bashir Ibrahim Idris ya halarci wannan taro ga kuma rahoton da ya hada mana.

An yi taro kan makomar arzikin Najeriya

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.