Isa ga babban shafi
Najeriya-Faransa

Makon nuna fina-finan Nollywood a Faransa

Angelique Kidjo shaharrariyar mawakiyar nan a cikin wani shirin fim
Angelique Kidjo shaharrariyar mawakiyar nan a cikin wani shirin fim © DR

Wannan shine karo na hudu a jere da juna da ake gudanar da makon nuna fina-finan Najeriya na Nollywood a birnin Paris na Faransa, bikin da aka fara tun a jiya alhamis za a ci gaba har zuwa ranar 5 ga wannan watan na yuni.

Talla

Daga cikin mahalarta wannan biki shine shugaban wannan harka ta fim a Najeriya baki daya Kunle Afolayan, wanda kuma fim dinshi ‘The CEO’ ke daga cikin fina finan da suka yi fice a bana, Afolayan ya nuna farin cikinsa ganin wannan shine karon farko da ake taba nuna sabon fim acikin jirgi, ganin an haska fim din ne a karon farko acikin  jirgin Air France da ya taso daga birnin Lagos a Najeriya zuwa birnin na Paris.

Masu harkar fina finai a  Najeriya da dama sun nuna farin cikinsu dangane da wannan bikin ganin yadda aka karrama kasar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.