Isa ga babban shafi
Najeriya

Buhari ya kaddamar rundunar yaki da 'Yan fashi a Zamfara

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kaddamar da rundunar yaki da 'Yan fashi a Zamfara
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kaddamar da rundunar yaki da 'Yan fashi a Zamfara saharareporters

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kai ziyara jihar Zamfara da ke arewacin kasar inda ya kaddamar da wani shiri na musamman na yaki da barayin shanu da suka dade suna cin karensu babu babbaka a jihar wajen kashe daruruwan mutane suna sace dukiyoyinsu.  

Talla

Shugaban ya kaddamar da runduna ta musamman da ta kunshi Sojoji da jami’an ‘yan sanda da kuma jami'an kare lafiyar fararen hula da za su shiga yaki da barayin Shanu

Rahotanni sun ce, tuni jami’an tsaron suka fara fitar da tsare-tsaren da za su yi amfani da su wajen kawo karshen kisan jama’a da yin garkuwa da su domin karban kudin fansa baya ga satar shanu da barayin ke yi a jihar.

Wannan matsalar ta sa daya daga cikin dattijan Jihar Sanata Sa’idu Dansadau a watan jiya ya bukaci shugaba Buhari da ya kafa dokar ta-baci a Zamfara da barayi suka addaba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.