Isa ga babban shafi
Najeriya

Gwamnan Zamfara ya yi watsi da batun tsige shi

Gwamnan Jahar Zamfara Abdulaziz Yari Mafara
Gwamnan Jahar Zamfara Abdulaziz Yari Mafara wordpress.com

Gwamnan jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya Abdulaziz Yari ya yi watsi da rade- radin da ake na cewar 'yan majalisar jihar na yunkurin tsige shi daga mukaminsa. 

Talla

Su dai 'yan majalisun sun gabatar da zarge- zarge guda 11 da suka hada da karkata akalar tallafin Naira biliyan 11 da aka karbo daga gwamnatin tarayya da kuma wata biliyan guda da aka karbo bashi daga babban bankin Najeriya  don inganta harkar noma.

Har ila yau 'yan majalisun na zargin gwamnan da rashin  zama a jihar don gudanar da ayyukan da suka rataya a wuyansa, baya ga zargin sa da bayar da umurnin kama shugaban majalisar da mataimakinsa da kuma shugaban masu tsawatarwa a zauren majalisar.

A hirasa da manema labarai gwamna Yari ya bayyana matakin tsige shi a matsayin wasan yara.

Muryar Gwamnan Zamfara Abdul-Aziz Yari

Sanarwar da ‘yan majalisar suka fitar sun yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari ya shiga tsakaninsu da gwamnan da ke amfani da jami’an farin kaya a matsayin barazana.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.