Isa ga babban shafi
Najeriya

Gwamnan Zamfara ya tsallake yunkurin tsige shi

Gwamnan Jihar Zamfara Abdulaziz Yari Mafara
Gwamnan Jihar Zamfara Abdulaziz Yari Mafara wordpress.com

Gwamnan jihar Zamfara da ke yankin arewa maso yammacin Najeriya, Abdulaziz Yari ya tsallake yunkurin tsige shi da majalisar jihar ta yi bayan sarakunan gargajiya da ‘yan siyasa sun shiga cikin lamarin.

Talla

Gwamna Yari wanda ke magana da manema labarai, ya bayyana cewa, ya gana da mambobin majalisar inda suka shawo kan matsalar rashin jituwa a tsakaninsu.

Zaman ganawar wanda shugaban jam’iyyar APC na jihar, Alhaji Lawal Kaura ya jagoranta, ya samu halartar daukacin sarakunan jihar da kuma ‘yan siyasa.

Kakakin majalisar Zamfara, Sanusi Garba Rikiji ya ce, Gwamna Yari ya amince da sharuddan da aka gindaya masa don kawo karshen barakar.

Rikiji ya bayar da tabbacin cewa, mambobin majalisar za su bai wa Gwanan taimakon da ya ke bukata, ina ya ce, sun gamsu da zaman sasanta su da sarakunan da ‘yan siyasar suka yi.

A cikin makwannin da suka gabata ne, ‘yan majalisar suka yi barazanar tsige shi bayan sun gabatar da zarge- zarge guda 11 da suka hada da karkata akalar tallafin Naira biliyan 11 da aka karbo daga gwamnatin tarayya da kuma wata biliyan guda da aka karbo bashi daga babban bankin Najeriya don inganta harkar noma.

Har ila yau 'yan majalisun sun zargi Gwamnan da rashin zama a jihar don gudanar da ayyukan da suka rataya a wuyansa, baya ga zargin sa da bayar da umurnin kama shugaban majalisar da mataimakinsa da kuma shugaban masu tsawatarwa a zauren majalisar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.