Isa ga babban shafi
Najeriya

Buhari ya jinjina wa shugaban Facebook

Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari da mataimakinsa, Yemi Osinbajo da kuma shugaban facebook, Mark Zuckerberg a birnin Abuja
Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari da mataimakinsa, Yemi Osinbajo da kuma shugaban facebook, Mark Zuckerberg a birnin Abuja naij.com

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya jinjina wa shugaban kamfanin sadarwa na facebook, Mark Zuckerberg game da kokarinsa na kara wayar da kan matasan kasar a fannin fasahar sadarwa.

Talla

Shugaban ya yaba wa Zuckerberg ne bayan ya gana da shi a fadarsa da ke babban birnin Abuja a yau Jumma’a.

Saukin kan Zuckerberg wanda shi ne na biyar wajen arziki a duniya ya kayatar da  Buhari, musamman yadda matashin ya cakudu da talakawan Najeriya a ziyar da ya kai.

A cewar shugaba Buhari, ba su saba ganin fitattun mutane kamar Zuckerberg na sassarfa a kan tituna ba har ta gai ga yin zufa.

A na shi bangaren, Mr. Zuckerberg mai shekaru 32 ya yaba da irin fasahar da matasan Najeriya ke da ita musamman a bangaren sarrafa kwamfuta  kamar yadda ya gani a garin Yaba da ke jihar Legas a kudancin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.