Isa ga babban shafi
Najeriya

Majalisar Dattawan Najeriya ta yi watsi da sunayen Jakadu 46

Sugaban Majalisar Dattawan Najeriya Sanata Bukola Saraki
Sugaban Majalisar Dattawan Najeriya Sanata Bukola Saraki

Majalisar Dattawan Najeriya, ta sa kafa ta shure sunayen Jakadu 46 da fadar shugaban kasar ta mika mata domin tantancewa.

Talla

Majalisar ta bukaci sake duba jerin sunayen jakadun 46 kashi na biyu kafin daga bisani a gabatar da su gabanta.

Majalisar Dattawan ta dauki matakin ne bayan kudurin da shugaban masu rinjaye na Majalisar Sanata Ali Ndume ya gabatar, wanda ya samu goyon bayan shugaban marasa rinjaye Sanata Godswill Akpabio.

A ranar 20 ga watan Oktoban da ya gabata, shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya bukaci Majalisar ta amince da sunayen Jakadun 46 kashi na biyu da ya aike mata.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.