Isa ga babban shafi
Najeriya

Jami'oin Najeriya na yajin aiki

Tambarin kungiyar malaman Jami'oin Najeriya wato ASUU
Tambarin kungiyar malaman Jami'oin Najeriya wato ASUU celestreet.com

A wannan Laraba ne malaman jami’oi na Najeriya ke fara gudanar da yajin aikin gargadi na tsawon mako guda, a wani mataki na janyo hankalin gwamnatin kasar don biya musu bukatunsu.

Talla

Shugaban kungiyar malaman, Biodun Ogunyemi ya bayyana bukatun nasu da suka hada da rashin aiwatar da yarjejeniyar da suka kulla a shekarar 2009 da 2013, wadanda suka kunshi bayar da isassun kudaden tafiyar da harkokin jami’oin da biyan malaman hakkokinsu da kuma daina amfani da tsarin asusun bai-daya a jami’oin.

Ogunyemi ya ce, daga yau Laraba babu koyarwa, ko jarabawa ko kuma halartar duk wani taro a daukacin jami’oin kasar.

A baya can jami'ion dai sun sha shiga yajin aiki, abin da ke haifar da jinkirin kammala karatu a kan kayyadadden lokaci ga dalibai.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.