Isa ga babban shafi
Najeriya

Obasanjo ya yi tsokaci kan salon mulkin Buhari

Tsohon Shugaban kasar Najeriya Olusegun Obasanjo
Tsohon Shugaban kasar Najeriya Olusegun Obasanjo AFP / Seyllou

Tsohon Shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo ya yaba da rawar da shugaban kasar mai ci Muhammadu Buhari ya taka wajen bai wa jami’an tsaro umurnin dirar mikiya kan manyan alkalan kasar da ake zargi da cin hanci da rashawa.

Talla

Obasanjo ya ce kama alkalan ya nuna kwarin gwiwar da bangaran zartarwa ke da shi wajen tsaftace bangaren shari’a da tuni cin hanci ya dabaibaye shi.

Tsohon shugaban wanda ya bayyana bangarorin da suka tabarbare da suka hada da Majalisa da kuma aikin gwamnati y ace duk da ya ke hanyar da aka bi wajen kama alkalan bai da ce, babu wata hanya ta dabam da za’a iya bi domin magance matsalar dole sai haka.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.