Isa ga babban shafi
Najeriya-Maiduguri

Mata 'yan kunar bakin wake biyu sun mutu a Maiduguri

Wajen da aka sami kunar bakin wake kwanan baya a garin Maiduguri
Wajen da aka sami kunar bakin wake kwanan baya a garin Maiduguri STRINGER / AFP

Wasu mata biyu ‘yan kunar bakin wake  sun kashe kansu a garin Maiduguri na jihar Borno dake Najeriya a lokacinda suke kokarin shiga wani massallaci da ake Sallah. 

Talla

Bayanai na cewa ‘yan kunar bakin waken ne kawai suka mutu yayinda mutane biyar dake Sallah suka jikkata a yankin Jiddari Polo dake Maiduguri.

Kakakin Rundunar ‘yan sandan jihar Borno Victor Isuku na cewa ‘yan matan sun so shiga masallacin ne amma Allah ya kare.

A ranar 23 ga watan Oktoba na shekara ta 2015  a wani masallaci dake kusa da wannan masallaci an sami harin kunar bakin wake irin wannan inda mutane 18 suka mutu.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.