Isa ga babban shafi
Najeriya

Kwale-kwale ya bace da mutane 150 a jihar Kebbi Najeriya

Masunta a kogin Argungu jihar Kebbi Najeriya a lokacin bukin kamun kifi na shekara ta 2008.
Masunta a kogin Argungu jihar Kebbi Najeriya a lokacin bukin kamun kifi na shekara ta 2008. Pius Utomi Ekpei/AFP/Getty Images via Boston pictures

Rahotanni daga jihar Kebbi a Najeriya na cewa wani kwale-kwale shake da mutane 150 ya bace,bayan  ya nutse a kogi dake Karamar Hukumar Ngaski.

Talla

Shugaban karamar hukumar Garba Hassan ya fadi cewa an sami gawan mutane 8 amma saura mutanen babu duriyar su.

Daya daga cikin wadanda suke cikin kwale-kwalen, wanda ya tsallake rijiya da baya,  ya fadi cewa suna tsakiyar tafiya jirgin  ya yi karo da wani abu a cikin ruwa.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.