Isa ga babban shafi
Najeriya-Kaduna

Kaduna: Dubban masu Sarautun gargajiya zasu iya rasa rawunansu

Masu rike da mukaman sarautun gargajiya sama da 3,000 na fuskantar barazanar rasa mukamansu.
Masu rike da mukaman sarautun gargajiya sama da 3,000 na fuskantar barazanar rasa mukamansu. observenigeria

Rahotanni daga jihar Kaduna a Najeriya sun ce, mai yiwuwa, masu rike da sarautun gargajiya akalla 3, 121, su rasa rawunansu.

Talla

Shawarar tana kunshe ne cikin rahoton kwamitin da gwamnan Kaduna Nasir El Rufa’I ya kafa don yin nazari, kan sauya fasalin tsarin mulkin sarautar gargajiya a jihar, ya mikawa gwamnati.

Kwamitin, ya bada shawarar soke Hakimai 194, Dagatai 2,927, sai kuma ‘Yan majalisar masarautun jihar 643.

Kwamitin ya kare kansa da cewa, ya bada shawara ce, kasancewar an kirkiro mafi yawancin mukaman Sarautun bisa dalilan siyasa, wanda kuma ware musu kudade ke sanya gwamnatin jihar Kaduna cikin tsaka mai wuya, idan aka yi la'akari da matsin tattalin arzikin da Najeriya ke fuskanta.

Yanzu haka dai akwai Hakimai 390, Dagatai 5,854, ‘yan majalisar masarauta 399, sai kuma ma’aikata 1,152 a cikin masarautu 32 da ke fadin jihar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.