Isa ga babban shafi
Najeriya

Najeriya ta fuskanci koma baya a kasuwanci tsakaninta da Birtaniya

Fashe-fashen bututun mai da durkushewar tattalin arziki ya shafi ribar kasuwancin Najeriya da kasar Birtaniya.
Fashe-fashen bututun mai da durkushewar tattalin arziki ya shafi ribar kasuwancin Najeriya da kasar Birtaniya. http://investorsking.com

A karon farko, cikin shekaru 7, Najeriya ta samu koma baya a fannin bunkasar kasuwanci tsakaninta da kasashen duniya, musamman kasar Birtaniya.

Talla

Ma’aikatar kididdigar Najeriya ta ce zuwa karshen shekarar 2016, kayayyakin da Birtaniya ke shigowa da su Najeriya, ya zarta yawan wadanda Najeriyar ke saida mata tun bayan shekara ta 2009.

Sabon rahoton da ma’aikatar kididdigar ta fitar, ya nuna cewa a karshen shekarar da ta gabata, Najeriya ta sayo kayayyakin da ake bukata daga Birtaniya, da darajarsu ta kai Naira biliyan 362, yayinda ita kuma ta saidawa kaya zuwa Birtaniyar da darajarsu ta kai, dala biliyan 300, abinda ke nuna Najeriya ta samu gibin akalla naira biliyan 62.

Masana tattalin arziki sun danganta koma bayan da Najeriya ta samu, da dalilai na durkushewar tattalin arziki, da kuma raguwar hako gangar danyen mai, da Najeriyar ta fuskanta a watannin baya, saboda fasa bututun mai da tsagerun yankin Niger Delta ke yi.

A shekara ta 2012, kididdiga ta nuna cewa, Najeriya ta samu ribar akalla naira triliyan 1 da biliyan 11, a tsawon shekaru shidda da aka kwashe na kasuwanci tsakaninta Birtaniya, kafin shekara ta 2016 da ta gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.