Isa ga babban shafi
Najeriya

Sojin Najeriya zasu fadada atasaye zuwa Kudu maso yammacin kasar

Wasu daga cikin jami'an sojin Najeriya yayin sintiri a yankin Panshekara nda ke jihar Kano, a ranar 19 ga watan Afrilu 2007.
Wasu daga cikin jami'an sojin Najeriya yayin sintiri a yankin Panshekara nda ke jihar Kano, a ranar 19 ga watan Afrilu 2007. REUTERS/Radu Sigheti

Rundunar sojin Najeriya ta ce zata kaddamar da fara atasayen da ta yi wa lakabi da "Operation Crocodile Smile", wato murmushin kada a Hausance, kuma atasayen sojin zai gudana ne a yankin Kudu maso kudancin kasar da kuma wasu daga cikin yankunan kudu maso yammaci.

Talla

Kakakin rundunar sojin Najeriya, Birgediya Janar Sani Usman Kuka Sheka, ya sanar da haka a ranar Asabar din data gabata.

Birgediya Janar sani Usman ya ce, bai kamata a rika sako siyasa cikin atsayen da sojin Najeriyar ke yi a sassan kasar ba, musamman ma kan wanda suka kaddamar a yankin kudu maso gabashin kasar, inda masu fafutukar kafa Biafra suka yi yunkurin tada yamutsi.

A cewar kakakin idan ba’a manta ba, a farkon shekarar da muke ciki, rundunar sojin ta gudanar da atasayen da ta yiwa lakabi da "Operation Harbin Kunama" a yankunan Arewa maso yammacin kasar da kuma arewa ta tsakiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.