Isa ga babban shafi
Najeriya

NLC ta nesanta kanta daga ikirarin durkusar da harkoki a Najeriya

Wasu ma'aikatan Lebura a jihar Legas da ke kudancin Najeriya, yayinda suke aikin loda cocoa cikin madaukan a za'a fitar da su zuwa kasuwannin kasashen turai.
Wasu ma'aikatan Lebura a jihar Legas da ke kudancin Najeriya, yayinda suke aikin loda cocoa cikin madaukan a za'a fitar da su zuwa kasuwannin kasashen turai. REUTERS/Thomas Ashby

Kungiyoyin kwadagon Najeriya, sun nesanta kan su daga ikrarin wata kungiya ta UCL, da ta yi ikirarin cewa a yau 18 ga Satumba zata durkusar da kasar saboda rashin yi mata rajista.

Talla

A makon daya gabata ne, kungiyar ta UCL, ta bukaci ma’aikata su tsunduma cikin yajin aiki, su kuma rufe tashoshin jiragen sama da na ruwa, yayinda ta gargadi jiragen waje da su kaucewa zuwa Najeriya, kana kuma suka bukaci mutane su tanadi abinda zasu ci daga yau, har sai abinda hali yayi,

A lokacin zantawarsa da Sashin Hausa na RFI, shugaban kungiyar kwadago ta NLC Ayuba Wabba ya ce lokaci yayi da dole kowa yabi doka da oda a Najeriya, ganin cewa an shiga yanayia kasar da wasu mutane ko kungiyoyi ke amfani da damar da suke da ita ta hanyar da basu dace ba.

Wabba ya kuma kara da cewa tun da fari ma Umarnin kungiyar haramtacce ne kasancewar dokar Najeriya ma bata san da ita ba.

NLC ta nesanta kanta daga kirarin durkusar da harkoki a Najeriya

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.