Isa ga babban shafi
Najeriya

An tsinto gawarwaki 16 bayan nitsewar kwale-kwale a Kebbi

Mutum 57 aka kiyasta na kan kwale-kwalen da ya nitse a Kebbi
Mutum 57 aka kiyasta na kan kwale-kwalen da ya nitse a Kebbi © Kyle G. Brown

An tsinto gawarwaki 16 cikin mutum sama da 50 da kwale-kwale ya nitse da su ranar talatan da ta gabata a garin Yawuri na jihar Kebbi da ke arewacin Najeriya.

Talla

Mutum 57 aka kiyasta na kan kwale-kwalen lokacin da ya nitse, inda aka samu damar ceto rayukan mutum 7 da gawarwaki 16.

A ranar talatan da hatsarin ya auku an gano gawarwaki 15 yayinda a jiya laraba kuma aka tsinto guda.

Masu aikin ceto na ci gaba da bincike sauran gawarwakin.

Wannan ba shine karo na farko da kwale-kwale ke kifewa da fasinjoji a Kebbi ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.