Isa ga babban shafi
Najeriya

Bankuna ba sa son mika kudin asusun ajiya ba bashi da BVN

Gwamnatin Najeriya ce ta bukaci kotu ta ba ta kudaden da ke cikin asusun da ba a yi ma rajista ba
Gwamnatin Najeriya ce ta bukaci kotu ta ba ta kudaden da ke cikin asusun da ba a yi ma rajista ba REUTERS/Afolabi Sotunde

Rahotanni a Najeriya na cewa bankuna da dama sun dukufa wajen neman ofishin ministan shari’ar kasar ya janye matakin da ya shirya dauka na kwace dukkanin kudaden da ke cikin asusun ajiya wadanda ba’a yi musu rijista ba (BVN).

Talla

Kafin wannan lokaci dai, babbar kotun Najeriya da ke zamanta a Abuja ta amince da bukatar da gwamnatin kasar ta gabatar mata, tana neman a rufe duk wani asusun ajiyar banki da bashi da rajistar lambar ta BVN.

Kotun ta kuma bayar da umarnin cewa dukkanin bankunan kasar su wallafa sunan duk wani asusun da ba’ayi wa rijistar tantancewa ba a jaridun kasar domin ya zama gargadi ga wadanda suka mallake su.

A halin yanzu dai mai shari’a Dimgba Igwe na babbar kotun tarayya da ke Abuja ya tsaida ranar 16 ga watan Nuwamba da muke ciki domin yanke hukunci na karshe a kan kwace kudaden da ke cikin asusun bankunan da ba a yi wa rijistar lamar tantancewa ta BVN ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.