Isa ga babban shafi
Najeriya

Jonathan ya bijirewa karbar sammacin kotu

Tsohon shugaban kasar Najeriya Goodluck Jonathan
Tsohon shugaban kasar Najeriya Goodluck Jonathan REUTERS/Afolabi Sotunde

Tsohon Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya bijirewa karbar sammacin kotu domin ba da shaida kan zargin cin hanci da rashawa da ake yi wa tsohon kakakin Jam’iyyar su ta PDP Olisa Metuh.

Talla

Ana tuhumar Metuh ne da karbar naira miliyan 400 daga hannun tsohon mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Kanar Sambo Dasuki daga cikin kudaden da aka ware domin sayen makaman yaki da kungiyar Boko Haram.

Metuh ya musanta zargin inda ya bukaci tsohon shugaban ya zama shaidar sa, amma duk kokarin mikawa tsohon shugaban sammacin kotu domin bada shaidar ta gagara, saboda yadda ya ke wasan buya da masu wasikar kotun.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.