Isa ga babban shafi
Najeriya

Najeriya: 'Yan kasuwa za su cigaba da sayarda litar mai kan Naira 145

Wasu 'yan najeriya, yayinda suke dakon samun damar sayen man fetur, a lokacin da ake fuskantar karancinsa a sassan kasar.
Wasu 'yan najeriya, yayinda suke dakon samun damar sayen man fetur, a lokacin da ake fuskantar karancinsa a sassan kasar. SundiataPost

Kungiyar 'yan kasuwa masu shigowa da kuma dakon man fetur na Najeriya sun amince da ci gaba da sayarda litar man fetur guda kan Naira 145, matakin da ya kawo karshen matsayar da ‘yan kasuwar suka cimma na cewa ba zasu iya ci gaba da sayarda litar man kan farashin gwamnati ba.

Talla

A ranar Talatar da ta gabata ne shugabancin kungiyar ‘yan kasuwar da ke shigar da man Najeriya, suka bayyana cewa ba zasu iya dorewa da farashin Naira 145, idan aka yi la’akari da farashin kudin Najeriyar kan kudaden ketare, musamman dala.

Bayan taron da ‘yan kasuwar suka yi a jiya Laraba da mambobin kwamitin da gwamnatin Najeriya ta kafa domin tattaunawa da su a karkashin jagorancin Karamin Ministan mai Ibe Kachikwu, sun cimma yarjejeniyar janye kudurin nasu.

Sai dai sun roki gwamnatin Najeriyar da ta biya su wasu kudade, da zasu rage musu gibin faduwar da suke samu a wajen shigo da tataccen man fetur din, bayan komawarsu aiki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.