Isa ga babban shafi
Najeriya

Kotu ta kori karar IPOB kan neman soke sanya ta cikin 'yan ta'adda

Shugaban masu fafautukar neman ballewar yankin arewa maso gabashin Najeriya, ya yinda ya ke sa'insa da wasu gandurobobi a farfajiyar babbar kotun Najeriya da ke Abuja.
Shugaban masu fafautukar neman ballewar yankin arewa maso gabashin Najeriya, ya yinda ya ke sa'insa da wasu gandurobobi a farfajiyar babbar kotun Najeriya da ke Abuja. REUTERS/Stringer

Babbar kotun tarayyar Najeriya da ke Abuja ta yi watsi da karar shugabannin kungiyar IPOB mai fafutukar kafa kasar Biafra, da ke bukatar kotun ta soke ayyana su da gwamnatin Najeriya ta yi a matsayin ‘yan ta’adda.

Talla

Yayin yanke hukuncin Mai shari’ah Abdul Kafarati, ya ce gwamnatin Najeriya ta cike dukkanin ka’aidojin da ya kamata, kafin mika wa kotun bukatar haramta kungiyar ta IPOB, dan haka babu inda aka sabawa doka.

Sai dai lauyen kungiyar ta IPOB Mr Ifeanyi Ejiofor, ya sha alwashin kalubalantar hukuncin a gaban kotun daukaka kara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.