Isa ga babban shafi
Najeriya

Gwamnatin Najeriya ta mayar da martani kan wasikar Obasanjo

Shugaba Najeriya Muhammadu Buhari
Shugaba Najeriya Muhammadu Buhari REUTERS/Shannon Stapleton

Gwamnatin Muhammadu Buhari a Najeriya ta mayar da martani kan wasikar tsohon shugaban kasar Cif Olusegun Obasanjo wanda ya bukaci kar shugaban ya nemi tazarce a zaben 2019.

Talla

Martanin da gwamnatin ta mayar a wata sanarwar da Ministan yadda labaran kasar Lai Mohammed ya fitar, ta ce neman wa’adi na biyu ba shi ne a gaban shugaban yanzu ba.

Jami’in gwamnatin ya ce babu laifi a wasikar tsohon shugaban, kuma sun ji dadin cewar ya fahimci nasarorin da suka samu a fanin yaki da cin hanci da rashawa da fanin tsaro, wanda ke cikin abubuwa 3 na yakin neman zabensu.

Ministan ya kuma ce da alama tsohon shugaban ayyuka sun masa yawa, shiyasa bai ga kokarinsu ba a fanin farfado da tattalin arzikin kasar wanda babu shaka sun fuskanci kalubali a wannan bangare amma yanzu komai na dai-daita.

Mista Lai ya ce akwai ‘yan Najeriya da dama da ke kiraye-kirayen neman shugaba Buhari ya yi tazarce wasu kuma na adawa, sai dai kuma abin da shugaban ya sanya a gaba yanzu shi ne yadda zai shawo kan matsalolin da kasar ke ciki ba takara ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.