Isa ga babban shafi
Najeriya

Cin amana ne a ce na kawar da kai a rikicin makiyaya- Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari REUTERS/Shannon Stapleton

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce, cin amana ne yadda ake ci gaba da fadin cewa, ya kawar da kai game da rikicin makiyaya da manoma na baya-bayan da ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama a johohin Benue da Adamawa da Taraba da Zamfara.

Talla

Shugaba Buhari ya bayyana haka ne a yayin tarbar tawagar kungiyar Kiristocin Najeriya, CAN karkashin jagorancin Archbishop Ignatius Kaigama a fadar gwamnatin kasar da ke birnin Abuja.

Buhari ya ce, yana iya kokarinsa wajen ganin cewa, hukumomin tsaro na cikin shirin ko-ta-kwana saboda girmar matsalar.

Shugaban ya kara da cewa, jami’an tsaro za su gurfanar da wadanda aka samu da hannu a rikicin da kuma wadanda aka kama dauke da makamai ba bisa ka’ida ba a yankunan da lamarin ya yi kamari.

Shugaban ya jaddada wa tawagar CAN cewa, tsarin da gwamnatinsa ta kawo na samar da filayen kiwon shanu, ba shi da nufin mallake wani yanki na Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.