Isa ga babban shafi
Najeriya

Rundunar sojin Najeriya ta kaddamar da sabon atasaye

Wasu jami'an sojin Najeriya cikin shirin ko-ta-kwana.
Wasu jami'an sojin Najeriya cikin shirin ko-ta-kwana. Pius Utomi Ekpei/AFP/Getty Images

Rundunar Sojin Najeriya ta kaddamar da wni sabon atasaye da ta yi wa lakabi da “Ayem Akpatuma” domin kawo karshen rikici tsakanin manoma da makiyaya, da kuma yawaitar sata da garkuwa da mutane a wasu jihohin arewacin kasar.

Talla

Shugaban sashin horarwa da aiwatar da ayyuka na rundunar sojin Najeriya Manjo Janar David Ahmadu ne ya sanar da daukar matakin, yayin zanatawa da manema labarai a Hedikwatar sojojin da ke garin Abuja.

Manjo Janar Ahmadu, ya ce atasayen zai fara ne daga 15 na watan Fabarairu, zuwa 31 na watan Maris, a jihohin, Benue, Taraba, Kogi, Nasarawa, Kaduna, da kuma Nija.

Kaddamar da atasayen ya zo ne bayan samun hasarar rayuka, a rikicin manoma da makiyaya da aka samu a jihohin da ke yankin tsakiyar Najeriya.

Manjo Janar Ahmadu ya ce a shekarar 2017 da ta gabata, Rundunar sojin Najeriya ta gudanar da makamancin atasayen a wasu jihohi na sassan kudanci da arewacin kasar, domin kara inganta tsaro a wuraren, kamar yadda kundin tsarin mulki ya bayar da dama.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.