Isa ga babban shafi
Najeriya

Jihar Kogi ta mika wa gwamnatin Najeriya fili mai fadin kadada 15,000

Gwamnan jihar Kogi Yahya Bello tare da Ministan ayyukan Noma na Najeriya Audu Ogbeh.
Gwamnan jihar Kogi Yahya Bello tare da Ministan ayyukan Noma na Najeriya Audu Ogbeh. Kogireports

Gwamnan jihar Kogi Yahya Bello, ya mika takardun mallakawa gwamnatin tarayyar Najeriya fili mai fadin kadada dubu 15,000 a jiharsa, domin amfani da shi wajen fara aiwatar da shirinta na samar da filayen kiwo ga makiyaya.

Talla

Yayin da ya ke mika takardun ga Ministan ayyukan noma na Najeriya Audu Ogbeh, gwamna Bello, ya ce jiharsa ta shirya jagorantar fara aiwatar da shirin na samar da filayen kiwon.

Gwamnan ya ce an samar da filayen ne daga kananan hukumomi biyu na jihar.

Fadin kadada dubu 10, an yanke shi ne a karamar hukumar Ajaokuta, sai kuma kadada dubu 5 da aka samar a karamar hukumar Adavi.

Gwamnan jihar ta Kogi, ya ce shi da al’ummarsa a shirye suke, da su rungumi makiyaya, manoma da kuma matasa, ta hanyar samar da kyakkyawan yanayi na zaman lafiya, da kuma tabbatar da nasarar dorewar shirin samar da filayen kiwon, domin kawo karshen rikice-rikicen da ake samu a baya bayan nan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.