Isa ga babban shafi
Najeriya

A shirye muke mu karbi tubabbun Boko Haram- Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari Sunday AGHAEZE / NIGERIA STATE HOUSE / AFP

Shugaba Muhammadu Buhari ya ce, gwamnatin Najeriya a shirye take ta karbi mayakan Boko Haram da suka amince su ajiye makamansu.

Talla

Shugaba Buhari ya bayyana haka ne a yayin kabar ‘yan matan makarantar Dapchi 105 da Boko Haram ta sako bayan ta sace su a fadarsa da ke birnin Abuja a wanann Jumma’a.

Shugaban ya ce, gwamnatinsa a shirye take ta gyara halayen tubabbun mayakan Boko haram tare da shigar da su cikin al’umma don ci gaba da rayuwa.

Buhari ya bukaci kowa da kowa da ya rungumi zaman lafiya don ci gaban Najeriya da mutanenta, yayin da ya gargadi ‘yan siyasar da ke neman cimma burinsu ta hanyar jefa jama’a cikin kunci.

“Gwamnati ba za ta amince da duk wani yunkurin mutum ko wata kungiya na sanya siyasa a sha’anin tsaro don cimma wasu muradun siyasa ba” In ji Buhari.

A bangare guda, shugaba Buhari ya lashi takobin ceto yarinya daya tilo ‘yar Dapchi da ke ci gaba da kasancewa a hannun Boko Haram bayan ta ki karbar addinin Islama kamar yadda rahotanni ke cewa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.