Isa ga babban shafi
Najeriya

Najeriya bata fuskantar tsananin hadarin sake bullar Ebola - WHO

Wasu jami'an lafiya na kungiyar likitocin kasa da kasa ta Medecins sans Frontieres (MSF), yayin aiki a wata cibiyar kula da masu fama da cutar Ebola, Kailahun da ke kasar Saliyo.
Wasu jami'an lafiya na kungiyar likitocin kasa da kasa ta Medecins sans Frontieres (MSF), yayin aiki a wata cibiyar kula da masu fama da cutar Ebola, Kailahun da ke kasar Saliyo. REUTERS/Tommy Trenchard

Hukumar kula da lafiya ta duniya WHO, ta ce Najeriya bata daga cikin kasashe masu fuskantar tsananin hadari na sake bullar cutar Ebola.

Talla

Sai dai cibiyar lura da kare yaduwar cutuka ta Najeriya da ta sanar da rahoton na hukumar WHO ta gargadi ‘yan kasar da su yi taka tsantsan wajen kula da matakan kare sake bullar cutar a kasar.

A watan Oktoba na shekarar 2014, WHO ta yi shelar cewa Najeriya ta kawo karshen cutar Ebola a kasar, bayan shafe kwanaki 42 ba tare da wani ya sake kamuwa da cutar ba.

A farkon makon da ya gabata ma’aikatar lafiya ta Jamhuriyar Dimokradiyar Congo ta tabbatar da sake bullar cutar Ebola a kasar, in da tuni ta hallaka mutane 17 a lardin Equateur da ke arewa maso yammacin kasar.

Karo na 9 kenan da ake samun bullar cutar ta Ebola a Jamhuriyar Dimokradiyar Congo tun a shekarar 1976.

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta ce, gwaje-gwaje da aka gudanar ga majinyatar na nuna cewar 2 cikin biyar na al'ummar kasar na dauke da alamun cutar.

Kusan shekaru 3 kenan bayan kawo karshen barkewar cutar Ebola a Afrika ta yamma, mafi muni a tarihi, bayanda ta hallaka sama da mutane 11,300, wasu kimanin 28,600 kuma suka yi fama da cutar a kasashen Guinea, Saliyo da kuma Liberia.

Lamarin dai ya faro ne daga kasar Guinea a watan Disambar 2013, bayan da wani yaro ya mutu sakamakon kamuwa da cutar, daga nan ne kuma ta bazu zuwa Saliyo da Liberia, daga bisani kuma cutar ta bulla a kasashen Najeriya, Spain, Amurka da kuma Birtaniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.