Isa ga babban shafi
Najeriya

"Hukumomi 15 sun karkatar da Naira triliyan 8 a zamanin Jonathan"

Ministan yada labaran Najeriya Lai Mohammed.
Ministan yada labaran Najeriya Lai Mohammed. REUTERS/Afolabi Sotunde

Ministan yada labarai da raya al’adu na Najeriya Lai Muhammed ya ce hukumomi 15 da ke samarwa kasar kudaden shiga, sun karkatar da naira triliyab 8.1 da ya kamata ace sun sanya a asusun gwamnatin tarayya.

Talla

Ministan ya sanar da bankado wannan badakala ce yayin gabatar da jawabi a birnin Osogbo na jihar Osun, wajen kaddamar da ayyukan yashe kogunan Ogbagba da Okoko.

Lai Muhammed ya ce an tafka badakalar karkatar da makudan kudaden ne a tsakanin shekarun 2010 zuwa 2015 a zamanin gwamnatin shugaba Goodluck Jonathan.

Munin karkatar da kudaden ya zarta wanda ya taba aukuwa a Najeriya a tsakanin shekarun 2006 zuwa 2013, inda binciken wani kamfani mai zaman kansa KPMG ya nuna cewa masu rike da manyan mukamai a kasar 55 sun sace naira triliyan 1.3.

Ministan yada labaran na Najeriya, wanda ya jaddada matsayin gwamnati mai ci kan kwato kudaden da aka sace, ya koka bisa cewar tilas Najeriya ta tsinci kanta cikin koma bayan ababen more rayuwa duba da cewa kudaden da aka karkatar ya kusan dai dai da kasafin kudin kasar na shekara guda.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.