Isa ga babban shafi
Bakonmu a Yau

Hon. Hamisu Shira kan amsa tambayoyi da Obasanjo zai yi akan Dala biliyan 16 da ya batar wajen gyara lantarki

Sauti 03:38
Shugaba Muhammadu Buhari tare da Olusegun Obasanjo.
Shugaba Muhammadu Buhari tare da Olusegun Obasanjo. nationaldailyng.com

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya bayyana cewa tsohon shugaban kasar Olusegun Obasanjo na da tambayoyin da zai amsa kan yadda aka kashe Dala biliyan 16 don gyaran lantarki ba tare da kwalliya ta  biya kudin sabulu ba lokacin mulkinsa.Buhari ya bayyana haka ne lokacin ganawa da kungiyar magoya bayan sa a karkashin shugaban hukumar kwastam, Kanar Hameed Ali da ta ziyarce shi.Wannan na zuwa ne bayan da Hukumar SERAP dake neman ganin an aiwatar da gaskiya a Najeriya ta bukaci babban mai shari’ar kasar ya kafa kwamitin bincike kan lamarin.Dangane da haka, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Hon. Hamisu Shira, tsohon dan majalisar wakilai, kuma ga yadda zantawar su ta gudana.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.