Isa ga babban shafi
Najeriya

Rundunar Sojin Najeriya ta musanta bacewar jami'anta

Wasu sojin Najeriya da ke yaki da Boko Haram
Wasu sojin Najeriya da ke yaki da Boko Haram AFP PHOTO/SUNDAY AGHAEZE

Rundunar Sojin Najeriya ta musanta rahotannin da ke cewa, dakarunta da motocinta sun bace bayan wani hari da kungiyar Boko Haram ta kaddamar mu su a garin Bama da ke jihar Borno.

Talla

Sanarwar da darektan hulda da jama’a na rundunar, Birgediya Janar Texas Chukwu ya fitar a ranar Litinin ta ce, babu kamshin gaskiya a labarin bacewar jami’an.

A cewar Chukwu, babu shakka ‘yan ta’adda na Boko Haram sun far wa sojojin a Kwakwa da Chingori da ke Bama, in da suka yi kokarin awon gaba da motocin dakarun amma aka fatattake su.

Mr. Chukwu ya kara da cewa, an yi nasarar kwance damarar mayakan Boko Haram 22, yayin da dama daga cikinsu suka samu rauni.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.