Isa ga babban shafi
Najeriya

Ubangiji ba zai yafe min ba idan na goyi bayan takarar Atiku - Obasanjo

Tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo.
Tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo. AFP PHOTO / SEYLLOU

Tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo, ya ce Ubangiji ba zai taba yafe masa ba, muddin ya goyi bayan takarar shugabancin Najeriya da tsohon mataimakinsa Atiku Abubakar ya ke nema.

Talla

Obasanjo ya bayyana haka ne a ranar Juma’ar nan da ta gabata, jim kadan bayan komawarsa Najeriya daga kasar Rwanda, yayin ganawa da jaridar Premium Times da ake wallafata a kasar.

Yayin ganawar Obasanjo ya ce kada ma tsohon mataimakin nasa Atiku Abubakar ya sa ran cewa zai samu goyon bayansa, a fafutukarsa ta neman kujerar shugaban Najeriya.

Kalaman na tsohon shugaba Najeriya, Obasanjo, sun zo makwanni biyu, bayanda Atiku Abubakar ya shelar aniyarsa ta neman jam’iyyar adawa ta PDP ta tsayar da shi takarar kujerar shugabancin kasar a zaben 2019 mai zuwa.

Wannan dai ba shi ne karo na farko da tsohon shugaba Obasanjo ke tayar da kura a fagen siyasar Najeriya ba, kasancewar a shekarar da ta gabata, ya rubuta budaddiyar wasika ga shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, inda ya ke shawartarsa da kada ya nemi wa’adi na biyu na shugabanci, bisa dalilai da dama da ya zayyana, wadanda ke sukar gwamnatinsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.