Isa ga babban shafi
Najeriya

Gwamnatin Legas ta bude gadar Third Mainland Bridge

Katafariyar gadar Third Mainland da ke birnin Legas a Najeriya.
Katafariyar gadar Third Mainland da ke birnin Legas a Najeriya. allAfrica.com

Gwamnatin Legas a Najeriya, ta bude babbar gadar da ta sada yankin tsibiri da kan tudun jihar ta kan ruwa, wato Third Mainland, wadda aka rufe ta a daren ranar Alhamis da ta gabata.

Talla

A yau Lahadi, 26 ga Agusta gwamnatin ta Legas ta sanar da cewa da misalin karfe 5 na yammaci za ta bude gadar.

An dai rufe katafariyar gadar ce, domin gudanar da bincike kan ayyukan sake karfafata da yakamata ayi, gwaje-gwajen da zuwa yanzu, injiniyoyi suka kammala, a cewar babban sakataren ma’aikatar Sufurin jihar ta Legas, Dakta Taiwo Salaam.

Rufe gadar na gajeren lokaci dai ya haddasa samun cinkoson ababen hawa, a hanyoyin da suka koma bi domin zirga-zirga tsakanin manyan yankunan kan tudu da kuma tsibirin da ke jihar ta Legas.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.